An fara aikin kai harin guguwar
Al-Aqsa ne bias jagorancin "Muhammad Zaif", babban kwamandan rundunan
Qassam.
A yau daidai lokacin da aka fara kai farmakin guguwar Al-Aqsa’ Aqassam ta kai hari da makamai masu kai kan wuraren makiya yahudawan sahyoniya.
Bataliyoyin Qassam na bangaren soji na Hamas, a ranar tunawa da fara kai farmakin Aqsa, sun kai hari a sansanin soji na Safa, da inda taron dakarun yahudawan sahyoniya a mashigar Rafah da kewayen garin Hawallit, da kuma Cibiyar aikin makiya a sansanin soji na Karam Abu Salem tare da rokoki masu gajeren zango 114 mm.
A sa’I daya kuma an smau Gagarumin hare-haren sojojin yahudawan sahyoniya kan zirin Gaza.
A daidai lokacin da ake ranar fara harin guguwar Al-Aqsa, sojojin yahudawan sahyoniya sun kai hare-hare a yankuna daban-daban na zirin Gaza, musamman arewacin wannan tsibiri, tare da kai munanan hare-hare.
A bangare guda shima an smau harin makamai mai linzami daga Lebanon zuwa arewacin Falasdinu da aka mamaye
Majiyoyi masu amfani da harshen yahudanci sun ba da rahoton wani harin roka da aka kai daga Lebanon zuwa wasu yankuna da ke arewacin Falasdinu da aka mamaye.
Bayan wannan harin an ji karar kararrawa hatsari a arewacin Palastinu da aka mamaye ciki har da Galili.
Har wala yau a yau din dai an harba rokoki 15 daga Lebanon zuwa Galili. Gidan rediyon sojojin yahudawan sahyoniya ya sanar da cewa, an harba makaman roka 15 a yankin Gabar Galili a zagaye na karshe na harin makami mai linzami da kungiyar Hizbullah ta kai kan yankin arewacin kasar Falasdinu.
Tashar talabijin ta 12 ta gwamnatin Sahayoniya ta kuma bayar da rahoton cewa, an harba makamin roka a yankin "Kasri Sami" da ke yankin Gabas ta Tsakiya. Hare-hare dai sai kara tsamari suke baya ga wanda yaki da ake fafatawa tsakanin sojojin yahudawa da dakarun Hizbullah a kudancin Labanon.
Bayanin Bayanai Wasu Sakamakon Da Guguwar Al-Aqsa Ta Haifar Ga Sahyoniyawan...
1. Matsanancin rikicin tattalin arziki da rashin aikin yi da guduwar masu zuba jari na kasashen waje daga kasuwancin da Isra’ila.
2 Samar da sabani da rashin jituwa karara a tsakanin mahukuntan gwamnatin Sahayoniya.
3. Raunan goyon bayan da kawancen gwamnatin da ke cin karensu babu babbaka daga wannan gwamnatin yahudawa.
4. Rashin tsaro a Palastinu da da Isra’ila ta mamaye.
5. Gurbacewar hare-haren yanar gizo akan tsarin gudanarwa, tsaro, tattalin arziki da ababen more rayuwaa Isra’ila.
6. Bayyanar bayanan sirri da tsaro.
7. Ikirarin shugabannin sahyoniyawan ga gazawarsa wajen tsaro da manufofin da y ace yana son cimmawa.
8. Amincewa da kudurin da ya haramta fitar da makamai zuwa sahyoniyawa a Majalisar Dinkin Duniya.